Labarai
An naɗa Ambasada Yunusa Hamza a matsayin Falakin Shinkafi
Masarautar Shinkafi a jihar Zamfara ta amince da naɗin Ambasada Yunusa Yusuf Hamza a matsayin Falakin Shinkafi.
Wannan na cikin wata sanarwa da Sarkin Shinkafi Alhaji Muhammad Makwashi Isah ya fitar a jiya Asabar.
Sanarwar ta ce, masarautar ta yi la’akari da irin ƙoƙarin da Ambasada Yunusa ke yi musamman wajen inganta rayuwar matasa.
A nasa ɓangaren Ambasada Yunusa Hamza ya yi godiya ga Allah bisa wannan karramawa da ya samu, inda ya ce hakan tamkar ƙaimi ne aka ƙara masa wajen ci gaba da ayyukan da ya sanya a gaba na wayar da kan matasa a Arewa.
You must be logged in to post a comment Login