Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sabon Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan ya kama aiki

Published

on

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yiwa mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar nan Usman Baba ado karin girma a matsayin mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda.

Karin girman na sa za zuwa ne yayin taron da ya gudana a Aso Villa da ke Abuja a Larabar nan.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayiwa sabon safeton, ta bakin ministan harkokin yan sanda, Mohammad Dingyadi a ranar Talata, wanda ya gaji Mohammed Adamu.

Tun da fari dai wa’adin tsohon sufeton yan sandan Muhammad Adamu ya kare tun a watan Fabrairun da ya gabata, bayan ya kammala wa’adin aikinsa na tsawon shekaru 35.

Sai dai daga baya ya samu karin wa’adin watanni uku daga Shugaban kasa, amma ya kwashe kimanin watanni biyu kacal daga cikin karin wa’adin watanni ukun da aka kara masa.

Rahoannin sun bayyana cewa tuni tsohon sufeton ‘yan sandan Muhammad Adamu ya mika aiki ga sabon sufeton Usman Baba ado a yammacin Laraba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!