Connect with us

Manyan Labarai

An raba sinadarin wanke hannu a Asibitin Murtala

Published

on

Shugaban kungiyar taimakon matasa ta Arewa, KuleChas Arewa kwamrade Abdullahi Aliyu ya yi kira  ga kungiyoyi  masu zaman kansu dasu taimakawa gwamnati a kokarin da take na  yakar cutar Corona.

Abdullahi Aliyu, yace kungiyoyi suna da rawar da zasu taka wajen taimakon  al’umma ba sai gwamnati  ka dai ba.

Abdullahi Aliyu ne ya bayyana haka lokacin da kungiyar su ta yi rabon  kayan wanke hannu da tsafatar sa a  asibitin Murtala.

Ya kara da cewa kungiyar su tana taimakawa asibiti da makarantun da kayan aiki kamar su sinadarin wanke hannu Sanitizer,  domin yakar cutar Corona mai lakabin Covid 19.

Labarai masu alaka.

Dalilan da suka sanya Buk ta musanta bullar cutar Corona

Covid-19: An takaita zirga-zirga a kasuwar kantin Kwari

Yace sun kuma shirya bita  don wayar da kan mutane akan cutar data gallabi  al’ummar duniya dama kasa baki daya.

A nasa jawabin shugaban asibitin Murtala,  Dakta Husaini Muhammad, ya yabawa wannan  kungiya, tare da yi musu alkawarin hadin kai tsakanin Asibitin da kungiyar , tare da gode musu da bisa bada tallafin  kayan wanke hannu.

Shamsu Dau Abdullahi, wakilin mu da ya halarci taron  ya rawaito cewa marasa lafiya da dama ne suka samu wannan tallafi na kayan a kokarin da ake na dakile wannan cuta mai saurin hallaka mutane.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

KAROTA ta kama babbar mota makare da giya

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce ta chafke wata mota makare da giya da darajar kudinta ya zarta miliyan 15.

Jami’an hukumar ta KAROTA ne dai suka bi motar da ke makare da katan din giya sama da dari uku, a kan titin Zaria da misalin karfe 3 na rana bayan da driben motar ya isa yankin Unguwar Sabon gari.

 

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na hukumar ta Karota Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, inda ta ce ko da jami’an na KAROTA suka lura direban motar hiya ya dauko ne kuma suka nemi dauki jami’an ‘yan sanda , wanda da tainakon su ne kuma suka cimma nasarar kame motar.

Direbobi sun maka KAROTA da ‘Yan sanda a gaban kotu

KAROTA ta baiwa jami’in ta kyautar kudi mai tsoka

KAROTA tayi wawan kamu a kasuwar Singa

Sai dai ya ce ko da Direban motar da sauran mutanen ciki suka lura jami’an ‘yan sanda da na KAROTA na bin su ne kuma suka tsere tare da barin motar a nan.

Sanarwar ta kuma kara da cewa duk jami’in Karotar da ya tallafawa jami’an tsaro wajen chafke mutanen da ke shigowa jihar Kano da muggan kwayoyi da kuma giya yana da kyauta mai tsoka.

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Kano ta fara feshin maganin cutar Covid-19

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za’a fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a Masallatai da Kasuwannin jihar Kano, inda ta ce dole ce ta sanya aka rufe hanyoyin shigowa jihar Kano ba wai son rai ba, kasancewar hakan na cikin hakan na cikin manyan hanyoyin hana shigowar cutar Covid-19 cikin kasar nan.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ne ya bayyana hakan jim kadan bayan shirin barka na nan freedom radiyo wanda mayar da hankali kan yadda gwamnati ta bada dokar rufe hanyoyin shigowa jihar nan da dokar zata fara aiki da misalign 12 na daren yau.

Kwamishinan ya kuma kara da cewar, rufe iyakokin jihar nan ne kadai hanyar da za’a bi wajen hana shigowar cutar Corona kasancewar cudanya da juna na cikin manyan hanyoyin kamuwa da ita.

A nasa bangaran kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Tsanyawa ya bayyana cewar gwamnatin tana gudanar da aikin Gyaran cibiyar kula da marasa lafiya ta ‘yar Gaya tare da kara inganta wasu daga cikin asibitici da kuma sanya kayayyakin kula da lafiyar a wani bangare na shirin ko ta kwana don yaki da cutar.

Kabiru Ibrahim Tsanyawa ya kuma bukaci al’umma da su kasance masu kula da tsaftar muhalin su tare da bin dokar da gwamnati ta gindaya, tare da bin shawarwarin likitoci da kuma kaucewa shiga cinkoson jama’a.

Continue Reading

Labaran Kano

Covid 19 a sanya dokar ta baci ga cutar-SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa Ilimi da al’amurran jama’a da Dumukoradiyya SEDSAC, ta yi kira gwamnatoci a dukkanin matakai da su rubanya kokarin su wajen yaki tare da kawo karshen cutar Corona Virus, mai taken Covid 19, tare da sanya dokar ta baci akan lamarin don ganin an samu dai daiton al’amurra nan ba  da dewa ba.

Shugaban kungiyar Kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa, ne ya yi wannan kiran a wata takarda da ya rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun sa.

Sanarwar ta kara dacewa rufe makarantu da ma’aikatu da kasuwanni, zai matukar kawo koma baya ga harkoki da dama musamman ma banagaren ilimi, don haka kungiyar ke kira ga gwamnatoci da su dau kwararan matakan cike gibin da ake samu a yanzu haka da sauran wasu bangarorin.

Labarai masu alaka.

Kungiyar kwadago ta bukaci a dau matakan Kariya na Corona

Covid-19: Kungiyar likitoci NMA ta raba kayan kare kai

Kungiyar ta SEDSAC, ta yi kira ga al’umma da subi matakai na kare kai da kuma bin dokoki sau da kafa da hukumomi suka gindaya tare da bin shawarwarin da likitoci da masu ruwa da tsaki akan harkokin lafiya,suka bayar  a gefe daya kuma tare da killace kai don kaucewa yada cutar, kasancewar al’umma nda muhimmiyar rawa da zasu taka wajen takaita yaduwar wannan annoba.

Bugu da kari kungiyar ta yi kira da al’umma da su gudanar da addu’o’i  da rokon Allah ya kawo karshen wannan annoba a kasar nan da duniya baki daya.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,348 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!