Connect with us

Labaran Kano

Covid-19: An takaita zirga-zirga a kasuwar kantin Kwari

Published

on

Kungiyar ‘yan kasuwar kantin kwari ta sanar da cewa ta mayar da lokacin shiga kasuwar daga karfe 10 na safe, sannan a tashi karfe 5 na yamma, daga yau Laraba.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Sharif Sagir Wada shi ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai, inda yace daukar matakan ya zama dole domin kaucewa annobar Coronavirus.

Sharif Sagir Wada ya ce, sun dauki tsa-ts-tsauran matakai da suka hadar rarraba abin wanke hannu a kowace kofa ta yadda duk wanda zai shigo sai ya wanke hannun sa.

Sannan kuma sun umarci dukkan ‘yan kasuwar da su tanadi abin wanke hannun, domin abokan hurdar su da kuma abin rufe baki da hanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!