Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An rufe wata makarantar sakandire a Kaduna

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe makarantar sakandiren ‘yan mata ta Kawo dake Kaduna, sakamakon ibitila’in gobara dake addabar makarantar.

Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna Malam Shehu Usman Makarfi ya shaidawa Freedom Radio cewa ibitila’in gobarar ta addabi makarantar  a ranar Asabar da ta gabata yayin da aka sake samun tashin sabuwar gobara da ta kama wani sashe na dakin kwanan daliban makaranta.

A don haka Kwamishinan ilimi na jihar ya ce ya zama tilas a rufe makarantar.

Shehu Makarfi ya ce an rufe makarantar ne har zuwa nan da mako biyu.

Labarai masu alaka:

An yi gobara a gidan Obasanjo

Gobara ta tashi a kasuwar GSM ta Alfin a Kano

Wakilin mu Haruna Ibrahim Idris ya rawaito cewa, hukumomin jihar ta Kaduna sun tattabatar da cewa, dakunan da gobarar ta lalata na daukar dalibai guda dubu daya da dari biyu da Ashirin.

Kwamishinan ilimin Malam Shehu Usman Makarfi yayi wa wakilin mu alkawarin cewa cikin wadannan makonni biyu ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna zata rarraba daliban zuwa sauran makarantun kwana dake jihar wadanda suka hadar data garin Soba, da Zaria da kuma Mararrabar Kubau, da ta Giwa da sauran su.

Sannan kwamishinan ya ce tuni ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna ta kafa kwamiti na musamman da zai binciko dalilan dake haddasa gobara a makarantar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!