Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Tashin kasuwar waya ta Farm center zai haifar da rashin aiki-shugaban kasuwar

Published

on

Shugaban kasuwar waya ta Farm Center da ke nan Kano, Malam Tjjjani Musa Muhammad, ya ce, matukar aka tashe su daga wajen da suke gudanar da kasuwancin su, to kuwa hakan zai kara ta’azzara matsalolin rashin aikinyi a jihar Kano

Malam Tijjani Musa Muhammad ya bayyana hakan ne bayan kammala shirin barka da hantsi na nan tashar freedom rediyo da ya gudana a safiyar yau.

Ya ce, ‘yan kasuwa da ke gudanar da sana’oinsu a kasuwar ta farm center, na kara kira ga gwamnati da ta taimaka musu ta janye matakin da ta dauka na tashin su daga wajen.

Malam Tijjani Musa Muhammad, ya kara da cewa, a shirye suke su bi duk wata doka da gwamnati ta shimfida musu.

Shugaban kasuwar sayar da waya ta Farm Center din ya kuma ce, tuni suka fara kiran ‘ya’yan kungiyar da suke kasuwancin waya da su kiyaye dokoki don samun wanzuwar zaman lafiya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!