Connect with us

Labaran Kano

An yi gobara a gidan Obasanjo

Published

on

Gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke garin Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Rahotanni sun ce da misalin karfe goma na daren jiya ne gobarar ta tashi a gidan tsohon shugaban kasar da ke Unguwar Ita-Eko a birnin Abeokuta.

Shaidun gani da ido sun ce, ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon tartsatsin wutar lantarki.

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Ogun, Fatai Adefala, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har yanzu suna binciken musabbabin tashin gobarar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!