Labarai
An sace mutane jama’a kusan 2000 tare da kashe wasu kusan 1500 a Najeriya a 2025 NHRC

Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya NHRC, ta ce, tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na shekarar da ta gabata, an sami aukuwar sace-sacen jama’a kusan 2000, aka kuma halaka wasu kusan 1500 a sassan kasar.
Jami’an hukumar ne suka bayar da wannan rahoto, a wajen wani taron tuntuɓa na kuniyoyin farar hula, kan halin da ake ciki game da batutuwan da suka shafi al’amuran kare hakkin bil’adama a kasar nan a birnin tarayya Abuja.
Rahoton ya ce an sace mutum 1712 sannan an kashe mutum 1463 a wurare daban-daban na kasar nan, daga watan Janairu zuwa watan Satumbar.
Hukumar kare haƙƙin bil’adaman ta kasa ta kuma yi tsokacin, cewa an sami ƙaruwar adadin yara ƙanana da aka yi watsi da su a rariya, inda a cikin watan Satumban da ya gabata aka lissafa aukuwar hakan har sau 2723.
BBC
You must be logged in to post a comment Login