Labarai
An sake samun katsewar wutar lantarki a Nijeriya
An sake samun katsewar wutar lantarki a ilahirin sassan Najeriya bayan durkushewar babbar tashar samar da wutar lantarki ta kasar a daren jiya laraba, matsalar da ke zuwa bayan TCN ta sanar da shafe akalla kwanaki 400 ta na fama da tangarda rarraba wutar lantarki a kasar mai yawan jama’a fiye da miliyan 200.
Kamfanin rarraba wutar lantarki ta Enugu EEDC ta ce ‘da misalin karfe 12 da mintuna 40 na dare ne lantarkin ya katse a tashar wanda ya jefa abokanan huldarsa a Abia da Anambra da kuma Imo baya ga jihar ta Enugu a duhu.
Haka zalika kamfanin lantarki na EKo a jihar Lagos ya sanar da katsewar wutar da misalin karfe 6 da mintuna 41 yayinda Kedco a jihar Kano ya tabbatar da wayar gari cikin duhu baya ga AEDC na Abuja.
Katsewar lantarkin na zuwa makwanni kalilan bayan kamfanin TCN ya sanar da bakar wahalar da su ke fuskanta wajen tafiyar da lantarkin kasar kari kan tulin matsalolin da bangaren na lantarkin Najeriyar ke fama da shi tsawon shekaru.
You must be logged in to post a comment Login