Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sake samun wata mata da ake zargi da auren maza biyu a Kano

Published

on

Kotun shari’ar musulunci dake zamanta a Hotoro, ta cigaba da sauraron karar da wani tsohon Dan Sanda mai suna Abubakar Abdullahi Sheka ya shigar gabanta, yana zargin matarsa tayi sabon aure akan auren sa.

Wannan tsohon Dan sanda ya bayyanawa kotun cewa, yana neman shari’a ta taimaka masa, ta kwato masa matarsa, mai suna Khadija Isah Musa, daga hannun makocinsa da suka zauna a gidan haya mai suna Muhammad Sani Dawaye.

Tun da farko mai kara Abubakar Abdullahi ya ce ya kwanta rashin lafiya ne sakamakon wani harin Bomb da ya rutsa da shi, a yayin da yake jinya ne kuma sai mai gidan da suke hayar ya basu wa’adin tashi daga gidan.

Ita kuwa matar Khadija Isah Musa ta ce ba zata bishi su koma gidansu na gado ba, karshe tilas ya barta a gidan.

Karin labarai:

Dalilan da suka sanya mace ta auri maza biyu a Kano

Hukumar Hisbah ta gana da saurayin dake shirin auren Ba’amurkiya

Sai dai kwatsam yana tsaka da zaman jiyya sai ga mahaifiyar matar ta zo har gida ta kawo masa katin daurin auren matar tasa da abokin zamansa a gidan hayar, sannan ta nemi da ya baiwa ‘yarta takardar saki, wanda shi kuma yaki aminta da hakan.

A yau ma dai kotun musulunci dake Hotoron karkashin mai shari’a Tijjani Yusuf Kademi ta zauna domin cigaba da sauraron karar, amma wadanda ake kara basu bayyana ba.

A don haka alkalin ya dage sauraron wannan kara har zuwa ranar 13 ga watan Maris da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!