Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mun sake bunkasa cibiyoyin bincike kan cutar Covid 19

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewar ta kara bunkasa cibiyar binciken nan da take kebe wadanda ake zargi na dauke da cutuka masu yaduwa dake ‘Yar Gaya a nan Kano, a wani mataki na dakile abkuwar cutar Corona a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai a yammacin yau, don yin kandagarki dangane da mummunar cutar Corona, da aka sauyawa suna zuwa COVID-19.

Wannan na zuwa ne, yayin da alkaluma ke nuna cewa fiye da mutane 2279 suka mutu a duniya baki daya, inda kuma aka tabbatar da bullar ta a jihar Lagos, da hakan yasa Nigeria ta zama kasa ta uku da aka samu bullar ta bayan kasashen Algeria da Egypt a nahiyar Afrika baki daya.

Kwamishinan lafiya Dr. Aminu Tsanyawa ya ce shakka babu akwai bukatar mutane su mayar da hankali kan yadda suke gudanar da harkokin rayuwarsu, tare da sanin inda za su shiga da kuma irin mutanen da za su yi mu’amala da su, don yiwa kan su kandagarki daga kamuwa da cutuka musamman ta COVID-19.

Yadda cutar Corona ta shigo Najeriya

Covid19: Babu dan kasar nan daya kamu da cutar Corona Virus.

Covid19: Gwamnatin Kano ta samar da lambobin kira kan Coronavirus

Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya kara da cewa ma’aikatar lafiya ta jiha a shirye take, biyo bayan kafa kwamitin karta kwana da zai rinka duba kai kawon rahotanni da suka shafi lafiyar al’umma, inda kuma ya bukaci mazauna jihar Kano da su kiyaye yada jita-jitar abubuwan da ba su tabbata ba, tare da kuma kai rahoton duk wani mutum da ake tunanin yana fama da matsananciyar rashin lafiya.

Wakilinmu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito cewa ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta bayyana cewar akwai bukatar da su kai rahoto idan aka samu mara lafiya da alamomin atishawa mai tsanani da kuma dagewa wajen kula da tsaftace hannaye, da kiyaye shiga taron al’umma mai yawa, da kuma yawan tafiye-yafiye ba gaira babu dalili tare kuma da kula da tashohin mota, dana layin dogo da kuma filin saukar jirgin sama.

Ma’aikatar lafiyar dai, ta ware layuka wayar tarho na karta kwana, domin mika rahoton duk wani yanayin rashin lafiya da mutane basu gamsu da shi ba. Lamobin sun hada da 08099973292 da 08039704476 da 08176677497 da kuma 08176673447.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!