Labarai
An samu karuwar masu kamuwa da zazzabin Lassa da kaso 57- NCDC

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta bayyana cewa an samu karuwar masu kamuwa da zazzabin Lassa da kaso 57 cikin mako guda, yayin da mutane 31 suka mutu cikin makonni biyar na farkon shekarar 2026. Sabbin wadanda aka tabbatar da cutar sun karu daga 28 zuwa 44 a mako na biyar, tare da bullar cutar a jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Plateau, Benue da Ebonyi, inda Bauchi ke kan gaba da yawan masu cutar.
A cewar rahoton, jihohi biyar, Bauchi, Ondo, Taraba, Edo da Plateau — su ne ke dauke da mafi yawan masu kamuwa da cutar. Mafi yawan wadanda cutar ke shafa matasa ne kasa da shekaru 21 zuwa 30.
Hakan ne ya sa aka kaddamar da matakan gaggawa tare da hadin gwiwa da kungoyoyin da hukumomin lafiya na duniyal, inda aka raba kayan kariya, magunguna da sauran kayayyakin jinya zuwa jihohin da cutar ta fi kamari.
You must be logged in to post a comment Login