Labarai
An samu katsewar Babban layin wutar lantarki na Najeriya

An samu katsewar babban layin wutar lantarki na Najeriya, lamarin da ya haddasa daukewar wutar a sassa da dama na Najeriya a yau Litinin, bayan da babban layin wutar lantarki na ƙasa ya faɗi, Inda ya jefa miliyiyin Mutane cikin duhu.
Bayanan da Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Ƙasa NISO ta fitar sun nuna cewa adadin wutar da ake samarwa ya tagu daga kusan megawatt 2,052 zuwa ƙasa da megawatt 140 cikin ƙasa da awa guda.
To sai dai har yanzu hukumar kula da wutar lantarki ta kasa TCN da Hukumar daidaita harkokin wutar lantarki NERC ba su fitar da wata sanarwa ba kan musabbabin katsewar wutar ko lokacin da ake sa ran dawo da ita.
You must be logged in to post a comment Login