Connect with us

Labarai

An samu raguwar hauhawar farashi da kaso 14 – NBS

Published

on

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa, NBS, ta ce hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan ta ragu zuwa kashi 14.63 cikin ɗari a watan Satumbar 2026, daga kashi 15.39 da aka samu a watan Agusta.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na ma’aunin farashin kayayyaki, wato Consumer Price Index, wanda ta fitar a Alhamis din nan.

Rahoton ya ce, Raguwar na nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a watan Satumba, duk da cewa hakan ba ya nufin farashin kayayyakin da ake saye a kasuwanni ya koma ƙasa kai tsaye.

Wannan na nufin cewa raguwar hauhawar farashi ba lallai ta kawo sauƙi ga masu ƙaramin ƙarfi ba, musamman waɗanda kuɗaɗen shigarsu ba su ƙaru ba, yayin da suke fuskantar tsadar abinci da sauran buƙatun yau da kullum.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!