Connect with us

Labarai

An gano gawar Sanata Bello Mandiya a gidansa da ke Abuja

Published

on

Majalisar dattawa ta ce,  an gano gawar Sanata Bello Mandiya a gidansa da ke birnin tarraya Abuja, kimanin sa’o’i 72 bayan rasuwarsa, ko da ya ke ana zargin cewa ya zame a bandaki ya faɗi tare da bugun kansa.

 

Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar mazabar Sanatoci ta Bauchi ta Tsakiya, ne ya bayyana hakan yayin zaman Majalisar Dattawa, inda ya ce maƙwabta ne suka gano gawar marigayin bayan wani wari ya fara fitowa daga gidansa.

 

A cewar Ningi, wari da ya fara tashi daga gidan ne ya jawo hankalin maƙwabta, musamman saboda an daɗe ba tare da an ga marigayin ba. Ana zargin cewa faɗuwar da ya yi a bandaki ce ta jawo rasuwarsa.

 

Sanata Ningi ya kuma bayyana cewa yana ƙasar Saudiyya lokacin da ɗansa ya kira shi ta waya domin sanar da shi rasuwar Bello Mandiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!