Kiwon Lafiya
An samu yamutsi kan rikicin sanya hijabi a jihar Oyo
Rahotanni na nuni da cewa an samu yamutsi sanadiyyar sanya Hijabi a jami’ar Fasaha Ladoke Akintola dake jihar Oyo.
An dai umarci kimanin dalibai 50 da suka shiga jami’ar sanye da Hijabi su cire ko a rufe su a jiya Litinin, kamar yadda wasu dalibai suka shaidawa manema labarai a garin Ibadan.
Lamarin da iya samo asali ne tun a shekarar 2011 bayan da muslmi suka nemi a basu damar sanya Hijabi a cikin makarantar kamar yadda addinin musulunci ya tsara.
Sai dai musulmin sun koka duba da cewa shekaru 8 kenan suna kiraye-kirayen amman babu wani mataki da hukumar makarantar ta dauka.
Tun daga wannan lokaci ne mata musulmi da suke halartar makarantar ke amfani da huluna domin rufe kawunan su wanda ya saba da koyarwar addinin musulunci.
Duk da cewar tsarin mulkin kasa ya baiwa kowa damar yin addinin sa, amman hukumar makarantar ta kawo tsaikon da suka kasa jurewa. A hudu ga watan Janairun nan ne musulmin suka yanke fara amfani da hijabin don cika umarnin addinin nasu