Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sanya ranar da za’a fara bada guraban karatu a kasar nan – JAMB

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB,  ta fitar da dokokin da shugabanin manyan makarantu za su bi wajen bada gurban karatu a makarantu su na zangon karatu na bana.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar Fabian Benjamin ya fitar cikin sanarwar da aka rabawa shugaban makarantu a jiya.

Ka zalika ta cikin sanarwar an umarci shugabanin su bai wa dalibai gurban karatu da suka nuna sha’awar su a gurbi na farko da na biyu wato first and second choices tun daga ranar 21 ga watan Agusta mai kamawa.

labarai masu alaka :

Majalisar wakilai ta gayyaci ministan ilimi kan rufe makarantu

Muna goyon bayan ilimi kyauta kuma wajibi -sabon Sarkin Kano

Har ila yau da yake jawabi a yayin taron manufofin hukumar na shekarar ta 2020, magatakardar hukumar  Ishaq Oloyede ya gargadi shugabanin da kada su take dokokin da aka shinfida musu wajen bada gurbin karatu a manyan makarantu na kasar nan.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!