Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

An sauke Chiroman Zazzau mai shekaru sama da 80 an ɗora ƙaninsa

Published

on

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya sauke Chiroman Zazzau Alhaji Sa’idu Mailafiya daga mukaminsa tare da maye gurbin sa.

Wata majiya mai tushe a masarautar ta ce, an sauke Mailafiya daga mukamin ne sakamakon halin rashin ɗa’a tare da rashin girmama masarauta.

Majiyar ta ce, har kusan sau shida Mailafiyan na nuna halin rashin ɗa’a ga Sarki a gaban jama’a, sannan an same shi da hannun wajen yunƙurin tunzura ƴaƴan masarautar domin yin bore ga Sarkin.

A saboda haka ne, masarautar Zazzau ta ce, ya zama dole ta ɗauki wannan mataki domin nuna masa cewa bai fi ƙarfin doka ba.

A wani ci gaban labarin kuma tuni Sarkin Zazzau ya amince da naɗin Alhaji Shehu Tijjani Aliyu Ɗan Sidi Bamalli hakimin Maƙera a matsayin sabon Chiroman Zazzau.

Wakilin Freedom Radio Hassan Ibrahim Zariya ya ce, a ranar Jumu’ar nan ne aka gudanar da naɗin sabon Chiroman a wani biki da aka gudanar a fadar Sarkin Zazzau.

Haka kuma Sarkin ya ɗaga likkafar ɗan uwan tsohon Chiroman Alhaji Shehu Mailafiya daga Makaman Gado da Masu zuwa Barden Zazzau.

Sannan Sarkin na Zazzau ya amin ce da naɗin Alhaji Halliru Nuhu Bamalli a matsayin sabon Makaman Gado da Masun Zazzau.

Dukkan canje-canje sun fito ne daga gidan Mallawa, wanda kuma aka naɗa su nan take.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!