Labaran Wasanni
An soke gudanar da gasar Tennis ta ATP da WTA
An soke gudanar da gasar Tennis ta ATP da WTA da zai gudana a kasar sin wato China sakamakon Annobar Corona.
Gasar wacce ta hada da ATP China Open da Shanghai Masters sai Chengdu Open da Zhuhai championship da ake sa ran gudanar dasu bana , ba zasu gudana ba bayan sanarwar da aka fitar ta soke su gaba daya.
Ita ma gasar WTA da mahukuntan ta sun soke gudanar da gasa guda bakwai wanda aka yi niyyar gudanar da su a bana, ciki har da wasan karshe ma WTA .
Soke wasannin ya biyo bayan sanarwar da mahukuntar kasar Sin China , suka bayar ta haramta gudanar da dukkanin wani wasa a kasar bana.
A jawabin sa , shugaban gudanar da gasar Andrea Gaudenzi, ya ce “A shirye suke su bi dukkan ka’idojin da suka dace musamman ma na mahukuntan kasashe , don haka muna girma ma matsayar kasar ta China da hukuncin da ta zartar”.
” Muna baiwa kowa da kowa hakuri tare da sanar muku da cewar gadar ATP bana ba zata gudana ba a kasar China , mungode wa masu shirya gasar da duk wani mai ruwa da tsaki”.Inji Gaudenzi.
Rahotanni sun tabbatar da cewar an samu mutum sama da miliyan 15, da suka kamu da cutar ta Corona , inda mutum dubu 600 da 30, suka Mutu a fadin duniya.
You must be logged in to post a comment Login