Connect with us

Labarai

An tsaida ranar jarabawar shiga NDA – Kwalejin horon hafsoshin sojojin Nigeria

Published

on

Za’a fara tantance masu sha’awar shiga makaranta ko kwalejin horas da hafsoshin sojoji ta kasa wato Nigerian Defence Academy a ranar 15 ga watan nan da muke ciki na Agusta.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da magatakardar kwalejin Brigadier Janaral A A  Aboaba ya sanya wa hannu cewa, za’a fara tantacewar da misalin karfe 7 na safe a cibiyoyin da aka kebe.

Ka zalika sanarwar ta umarci dukkanin dalibai su zo da katin samun gurbi na NDA da slip na UTME da hotuna guda biyu  da takardun da suka zabi kwasa-kwasan da suke sha’awa.

Har ila yau, an umarci dukkanin dalibai da su sanya takunkumin fuska da yin ta’azara duk dalibin da bai sanya ba, ba za’a bar shi ya shiga dakin jarrabawar ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!