Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kashe mace mai ciki da ƙanwarta a Kano

Published

on

⦁ Wani magidanci Malam Sagir mai magani ya tarar da gasar matarsa da kanwarta bayan ya dawo gida da misalin 11 na dare.

⦁ Lamarin ya faru a unguwar Rijiyar Zaki Fadama inda mai gidan ya tarar da kofar gidan a bude.

⦁ Hakan ya sanya ya fito a guje tare da sanar da makotansa abinda yake faruwa ne, kuma suka sanar da rundunar ‘yan sanda

Lamarin ya faru a unguwar Rijiyar Zaki Fadama inda mai gidan ya tarar da kofar gidan a bude.

Hakan ya sanya ya fito a guje tare da sanar da makotansa abinda yake faruwa ne kuma suka sanar da rundunar ‘yan sanda.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaidawa Freedom Radio cewa yanzu haka sun kama yaron da ake zargi da kisan mai suna Gaddafi Sagir tare da mai gidan domin gudanar da bincike.

Mai gidan dai ya tarar da gawarwakin a kwance cikin jini a kofar ɗaki inda ita kuma yarinya a kan kujera an shaƙe wuyanta da ɗan kwalin atamfa.

Tag: Rundunar ‘yan sanda Jihar Kano. Freedom Radio. Salisu Baffayo. Shamsiyya Farouk Bello.

.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!