Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bijilanti sun kashe ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Sumaila

Published

on

⦁ Kwamandan bijilanti na karamar hukumar Sumaila ya ce sun samu kiran waya da misalin karfe ukun dare kan wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sunje yankin.

⦁ ‘Yan bijilantin sun samu nasarar tarwatsa masu garguwa da mutanen, inda suka ji wa wasunsu ciwo, tare da kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen.

⦁ Ya zuwa yanzu dai gawarsa na wurin ‘yan sanda don gudanar da bincike.

A dare jiya Asabar ne jami’an Bijilanti dake karamar hukumar Sumaila suka samu nasarar harbe Ali gomo Wanda ake zargin ya Jima Yana yin garkuwa da mutane a yankin.

kwamandan bijilanti na Sumailar Alhaji Wada Muhammad ne ya bayyana hakan ga wakilin Freedom Radio, Yusuf Ali Abdallah.

Alhaji Wada Muhammad ya ce da misalin karfe na dare ne aka kira su aka shaida musu cewa wasu sun zo da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka je gidan wani ‘dan kasuwa mai suna Alhaji Dahiru.

‘Hakan tasa Jami’ansu suka isa wannan wurin, inda su ka yi dauki ba dadi da maharan, a nan ne suma jami’an na bijilanta suka yi amfani da bindiga Mai alburushi suka jikkata wasu tare da halaka guda mai suna Ali gomo’.

Kwamandan ya ce daga bisani ne aka dauki gawar Ali gomo zuwa sharkwatar ‘yan sanda na wannan yankin don zurfafa bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!