Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An yi garkuwa da mutane a Zamfara

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutane huɗu tare da sace dukiya mai yawa a garin Nahuce na ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara.

Wakilin mu Bashir Sharfadi ya zanta da sarkin garin Alhaji Sule Marafa Nahuce wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Sarkin ya ce, ƴan bindigar sun shiga garin ne da safiyar yau Litinin inda suka sace mutane huɗu, waɗanda har zuwa wannan lokaci ba a san inda suke ba, kuma ba a samu koda kiran waya daga wurin ƴan bindigar ba.

Ya ƙara da cewa, ƴan bindigar sun kuma ƙwace kuɗaɗe waɗanda har zuwa yanzu ba a tantance adadinsu ba a hannun wani babban ɗan kasuwa a garin mai suna Alhaji Ibrahim Mai Shago.

Freedom Radio ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Zamfara, SP. Muhammad Shehu wanda ya ce, zai yi mana ƙarin haske a kai da zarar ya isa ofishin sa, sai dai har zuwa wannan lokaci ba mu samu ji daga gare shi ba, duk da cewar mun sake tuntuɓar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!