Connect with us

Labarai

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon kazamin hatsarin mota a Kano

Published

on

Mutane 11 ne suka rasa rayukan su a wani mumunan hatsarin mota da ya afko da safiyar yau a nan Kano.

Hatsarin ya afko ya afku ne da misalin karfe 11 da rafe na safiyar yau a dai-dai kauyan Tsaida dake karamar hukumar Gaya a nan Kano.

Wani ganau Alhaji Yahaya Adamu y ace hatsarin ya afku ne bayan da aka rufe hannu daya na titin da ake bi kuma motocin na bin hannu daya.

A cewar Alhaji Yahaya Adamu motar da yi tahu-mu-gama  yayin da hatsarin ya afku.

Ka zalika  ganau din ya ce cikin mutane 11 da suka rasa rayukan su akwai kananan yara biyu da mace guda da kuma maza 8.

Sai dai daga nan Freedom Radio mun tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kano, amma hakan mu bai cimma ruwa ba.

Muna dauke da cikakken labarin cikin labaran duniya na Freedon radio

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,998 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!