Connect with us

Labarai

Mutane sun rasa rayukan su a wani hatsari a Kano

Published

on

An tabbatar da mutuwar mutum biyar yayin da mutum 4 suka sami munanan raunika a wani hatsarin mota da afku akan hanyar Rano zuwa garin Dan Hassan cikin karamar hukumar Kura.

Jami’in yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Alhaji Sai’du Mohammed ya tabbatar da afkuwar hadarin ga manema labarai  a yau Alhamis.

Alhaji Sai’du Mohammed ya ce hadarin ya afko ne da misalin karfe 8 da minti 49 yayin da wata motar safa ta haya suka yi taho mu gama da babur mai kafa uku wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutune 5.

Kazalika jami’in yada labarai ya ce ana zargin cewa direban na gudun wuce sa’a ya yin da hadin ya afko.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!