Connect with us

Labarai

Hatsarin babur ya raunata mutane a Kano

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce an samu afkuwar wani hatsari a dai-dai gadar sama ta Aminu Dantata dake titin Murtala Muhammad a nan Kano.

Hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 10:20 na daren Litinin ya afku ne ga wasu matasa biyu dake kan babur mai kafa biyu, wanda su ka ci karo da wani gini dake raba tsakiyar titi.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Kano Sa’id Muhammad Ibrahim ya shaidawa Freedom Rediyo cewa, bayan da su ka samu labarin, sun aika da jami’an su wanda suka dauki matasan guda biyu da su ka samu raunuka zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Freedom Radio cewa kaucewar ginin titin daga muhallin sa shi ne ya haifar da afkuwar hadura a wurin.

“Da rana ma wata mota tayi hatsari da ginin, amma daga baya aka dauke ta daga wurin” a cewar wani daga shaidun gani da idon.

Sai dai kakakin hukumar kashe gobarar ta Kano ya ce suna cigaba da bincike domin tabbatar da musabbabin abun da ya haifar da hatsarin.

Karin labarai:

Mutane sun rasa rayukan su a wani hatsari a Kano

An yi hatsarin mota har sau uku a titin Sharada

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!