ilimi
An yi wa kwamitin ciyar da ɗaliban Kano garambawul
Gwamnatin tarayya ta yiwa kwamitin kula da harkokin ciyarwar ɗalibai a jihar Kano garambawul.
Ta yadda a yanzu zai bada dama wajen sanya idanu sosai a ɓangaren ciyar da ɗalibai abinci a makarantun jihar Kano.
Ministan jin ƙai da kare abkuwar ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan shirin ciyarwar ɗaliban kano tare da ƙaddamar da kwamitin da zai kula d harkokin ciyarwar.
Ministar wadda ta samu wakilcin mataimakinta na musamman Abubakar Ibrahim Hashim ya ce “mun samu rahoton yadda ake tafiyar da harkokin ciyar da ɗalibai abinci a makarantun firamare na gwamnati a Kano, wannan ne ya sanya muka zo domin yin garambawul ga shirin kuma muna buƙatar sanya tsoron Allah a lamarin domin kuwa dukkanin waɗanda ake ciyarwar yaran mu ne”.
“Idan yaran mu sun samu abinci mai kyau ilimin su zai bunkasa kuma za su samu kyakyawar rayuwa” a Cewar ministan.
An ƙaddamar da kwamitin da zai riƙa kula da harkokin ciyar da ɗaliban Firamare na jihar Kano abinci, domin inganta harkokin koyo da koyarwa.
You must be logged in to post a comment Login