Labarai
An yi watsi da bukatar ma’aikata yayin tsara dokar Haraji – NLC

Shugaban Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Comrade Joe Ajaero, ya bayyana damuwa kan sabuwar dokar haraji, yana mai cewa an yi watsi da bukatar ma’aikata yayin tsara dokar, lamarin da ya kara nauyi ga masu karamin karfi. Ya ce harajin da ya shafi albashin mafi karanci ba adalci ba ne kuma yana tilasta wa talakawa karin nauyi.
Ajaero ya gargadi gwamnati da kada ta cigaba da aiwatar da dokar ba tare da gyara ba, yana mai cewa ci-gaba da hakan zai iya rage amincewar jama’a da kawo barazana ga tsarin dimokuradiyya. Ya ce dokar tana nuna cewa ma’aikata da talakawa sun kasance a waje yayin yanke hukunci mai tasiri a rayuwarsu.
Ya kuma jaddada cewa dimokuradiyya ba ta tsaya ga zabe kawai ba; tana bukatar mutunta doka, inganta hukumomi, da gwamnati mai hidima ga al’umma baki daya. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba dokar domin tabbatar da adalci ga kowa.
You must be logged in to post a comment Login