Connect with us

Ƙetare

An yi yunkurin juyin mulki a Burkinafaso

Published

on

Gwamnatin soji a Burkina Faso ta ce ta dakile wani sabon yunkurin juyin mulki da aka shirya domin hambarar da shugaban kasar na rikon kwarya, Kanal Ibrahim Traoré. Ministan tsaro, Mahamadou Sana, ya bayyana cewa an dakile shirin ne a daren Asabar sakamakon aikin kwararrun jami’an leken asiri.

Gwamnatin ta zargi tsohon shugaban rikon kwarya, Paul-Henri Damiba, da shirya yunkurin, inda ta ce an tsara hallaka shugaban kasar da wasu manyan jami’an soja da fararen hula, ta hanyar harbi ko dasa bam a gidansa. Damiba dai shi ne Traoré ya kifar da shi a juyin mulkin watan Satumban 2022.

Ministan ya kara da cewa an gano shirin ne bayan samun wani bidiyo da ke nuna masu kitsa yunkurin suna tattauna shirin, yana mai zargin cewa an samu tallafin kudi daga kasar Ivory Coast, tare da shirin kai hari kan sansanin tashi da jiragen drone kafin kasashen waje su iya shiga tsakani kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!