ilimi
An zabi Farfesa Chris Piwuna a matsayin sabon shugaban ASUU

Kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU ta za bi Farfesa Chris Piwuna babban likita a Asibitin koyarwa na Jami’ar Jos da ke jihar Filato a matsayin sabon shugaban ta.
Farfesa Piwuna, ya karbi shugabancin kungiyar ne daga hannun Victor Osodeke da ke jami’ar koyar da aikin Noma ta Michael Okpara da ke jihar Abia.
Nadin nasa ya biyo bayan taron da masu ruwa da tsaki a kungiyar suka gabatar karo na 23 da ya gudana a birnin Benin da ke jihar Edo.
An dai kada kuri’a ne tsakanin Farfesa Piwuna da Farfesa Adamu Babayo na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.
You must be logged in to post a comment Login