Labarai
Ana bata yaren Hausa a yayin yin tallace-tallace- Marubuta
- Anyi kira ga kungiyar marubuta dasu sanya ido akan masu yin tallace-tallace, wajen tabbatar da ana amfani da dai-daitacciyar hausa.
- Yawwancin harsuna suna amfani da yaren su ne, wajen gudanar da talla a yankunan su.
- Iyaye su daure su karanta wannan littafin, don gyara tarbiyar iyalansu.
- Marubuciyar ta rubuta littafin ne don gyaran tarbiyar al’umma.
Wani marubuci a Kano yayi kira ga kungiyar marubu ta, da hukumar dake kula da tallace-tallace karkashin jagorancin masana yaren Hausa da su sa ido wajen ganin ana amfani da dai-daitacciyar hausa a Kano.
Sagiru Sani Ahmad ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da littafin ‘Makomar mu’ da marubuciya Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta rubuta, wanda ya kunshi matsalolin da kasar hausa take fuskanta a yanzu.
Sagiru Sani Ahmad ya ce akwai harsu nan da da dama a yanku nan su, suna amfani da yarensu ne wajen yin talla, don bunkasar wannan yaren, wanda kuma doka ce kan a yi talla yadda yake a yaren, sai dai kuma anan Kano ba haka abin yake ba.
A hannu guda tsohon wakilin karamar hukumar birnin Kano, Alhaji Aliko Shu’aibu Mukhtar cewa yayi ‘wannan littafin zai taimaka wajen gyara tarbiya, musamman ma idan iyaye zasu daure su karanta shi.
Ita kuwa marubuciyar littafin Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo cewa tayi ‘ta rubuta littafin ne kan yadda tarbiya ta koma a yanzu, da kuma hanyoyin gyarawa’.
Wacce ta ce, ‘ana sa ran wannann littafin ya zamu daya daga cikin jadawallin littattafan da ake amfani dasu a makarantun jihar Kano’.
You must be logged in to post a comment Login