Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Freedom

Ba za mu bari ayi amfani da miyagun kwayoyi yayin babban zabe ba-NDLEA

Published

on

  • Ba zamu bari ayi amfani da miyagun kwayoyi a babban zaben kasa da ke tafe ba
  • Duk wanda muka kama da shigo da kwayoyi za’a kama shi
  • Duk wanda ta kama kuma yana shaye-shaye shima za’a kamashi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen Jihar Kano, ta ce, ba za ta bari ayi amfani da miyagun kwayoyi a babban zaben kasa da ke tafe ba’.

Shugaban hukumar Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radiyo.
Ya ce, za su yi amfani da hanyoyin ba sani ba sabo akan duk wanda aka kama da shigo da kwayoyi, ko raba su a waje kafin zabe da lokacin zabe za ta kama shi.

Kwamandan Abubakar Idris ya kara da cewa hukumar bazata saurarawa duk wanda ta kama yana shaye-shaye ba, ta hanyar kama su, tare da hukunta su dai-dai da laifinsu.

RAHOTO: Hafsat Abdullahi Danladi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!