Labarai
Ana cigaba da kai hare-haren jihar Zamfara,yayin da gwamna ya shafe kwanaki baya jihar
A yayin da ake cigaba da kai hare-hare wasu daga cikin yankunan jihar Zamfara, Gwamnan Abdul’aziz Yari ya kwashe wasu ‘yan kwanaki baya cikin jihar.
Fiye da mutane 40 ‘yan bindiga da masu satar shanu suka kashe a cikin makwanni 2 kadai a wasu daga cikin kwananan hukumumin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewar, gwamnan kafin barin sa jihar ya mika ragamar harkokin jihar ga kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Sunusi Garba Rikiji maimakon mataimakin sa Alhaji Ibrahim Wakkala Mohammed wanda yake jihar.
Sai dai ana zargin cewa dangantaka ta yi tsami a tsakanin gwamnan da mataimakin sa.
Da manema labarai suka tambayi kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Muhammad Danjari Kotorkoshi kan dalilin da yasan ya gwamnan ya dauki wannan mataki, ya ce mai son cewa komai akan wannan zancen.
Kawo yanzu gwamnan bai bayyana a jihar ba duk da matakin da gwamnatin tarayya ta baiwa babban hafsan sojan sama na ya koma jihar don kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.