Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana fargabar rasa rayuka tare da jikkatar sama da mutane 50 sanadiyyar gobara a Kano

Published

on

Ana fargabar an samu asarar rayuka tare da jikkatar sama da mutane 50 a wata gobara da ta tashi a Kano.

Shaidun gani da ido sun shaidawa Freedom Radio cewa, gobarar ta tashi ne da yammacin yau Asabar, a gidan man Al-ihsan da ke unguwar Sharaɗa.

Hukumar kashe gobara ta tarayya reshen jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’in yaɗa labaran ta ASF. Nura Abdulƙadir Me Gida.

Ya ce, yanzu haka sun kashe gobarar inda suke garzaya wa da waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.

A ziyarar da Freedom Radio ta kai asibitin Murtala ta iske sashen bada agajin gaggawa na asibitin cike da dandazon jama’a.

Freedom ta kuma iske yadda ake zaunar da wasu da al’amarin ya shafa a kan tantangaryar simintin asibitin cikin mawuyacin hali.

A gefe guda jami’an lafiya na ci gaba da bada kulawa ga waɗanda lamarin ya shafa.

Kwamishinan lafiya na Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ziyarci asibitin domin ganewa idon sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!