Kiwon Lafiya
Ana iya daukar cutar Corona ta iska – WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akwai shaidun dake nuna cewar ana iya daukar cutar Covid-19 ta iska, sakamakon binciken da wasu masana kimiyya suka yi, wanda ke nuna cewa kwayar cutar na iya tafiya fiye da minti biyu a iska kafin ta fadi.
Babbar Jami’a a hukumar Farfesa Benedetta Allgranzi ce ta sanar da wannan sabon rahoto, inda ta ce sun tabbatar da wannan sabon binciken, saboda haka yana da muhimmanci mutane su fahimci wannan sabon bincike domin kiyaye wa.
Binciken da masana kimiyar 239 suka yi a duniya, ya ce cutar na iya tafiya fiye da mita biyu, lokacin da wanda ya kamu da ita ya numfasa ko kuma ya zubar da wani ruwa daga jikin sa.
Kafin wannan lokaci dai, hukumar ta ce ana yada wannan cutar ne sakamakon mu’amala tsakanin mai dauke da ita, abinda ya sa aka bukaci bayar da tazarar akalla mita biyu tsakanin jama’a wajen hulda yau da kullum.
You must be logged in to post a comment Login