Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana kace-nace kan matsayin ‘Farfesa’ ga Ganduje

Published

on

Jami’ar East Carolina (ECU) da ke ƙasar Amurka ta musanta bai wa gwamnan Kano aikin koyarwa da kuma Farfesa.

Rahoton jaridar Premium Times ya rawaito jami’ar na cewa wasiƙar da wani ma’aikacinta ya aike wa gwamnan ba ta da amincewar hukumar jami’ar.

A ranar 1 ga watan Disamba ne sakataren yaɗa labaran gwamna Ganduje ya bada sanarwar cewa jami’ar ta naɗa gwamnan a matsayin Farfes tare da ba shi aikin koyarwa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje lokacin kulla wata yarjejeniya da wani kamfanin kasar China kan tattara haraji a shekarar 2017.

Sai dai sanarwar da jami’ar ta fitar a baya-bayan nan ta rushe wannan batu.

Freedom Radio ta tuntuɓi sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano sai dai ya ce ba a bashi iznin yin magana ba.

Al’umma na ta cecekuce a kai

Tuni al’umma suka shiga bayyana ra’ayoyinsu a kai, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun riƙa amfani da maɓallin Hash Tag da suka kira #VisitingFarfesaChallenge.

Ga wasu cikin masu yin tsokaci a kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!