Labarai
Ana shagulgulan karamar sallah yau a Nijar
Al’ummar jamhuriyar Nijar sun bi sahun takwarorin su daga kasashen musulman duniya wajen shagulgulan salla karama.
A jiya ne dai majalisar musulunci ta kasar ta fitar da sanarwar ganin jinjirin watan a wasu sassan kasar wanda hakan ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadan.
Tun da sanyin safiya ne dai al’ummar musulmin kasar suka yi fitar dango dan halartar masallatan idi.
Da misalin karfe 9 na safe ne, Limamin babban masalacin Idi ya jagoranci sallah raka’a biyu kamar yadda addinin musulunci ya tanada kafin daga bisani ya gabatar da huduba da harshen larabci.
Bayan haka suma daya bayan daya gwamnonin jihohi da mai martaba sultan na Damagaram sun gudanar da wani takaitaccen jawabin barka da salla ga al’ummar jihar.
Wannan sallah dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da cutar Covid-19 lamarin kuma da ya rage armashin sallar masamman ga magidanta da ke kukan rashin kudi.
Wakilinmu Yakuba Umaru Maigizawa ya rawaito mana cewa za’a ci gaba da bukukuwan karamar sallar har nan da kwanaki uku masu zuwa kamar yadda aka saba a al’adance.
Ku kalli hotunan yadda sallar idi ta kasance:
You must be logged in to post a comment Login