Labarai
Ana yiwa Ƴan Soshiyal Midiyan APC shaguɓe kan taron Tinubu a Jos
Dandalin sada zumunta na Facebook ya cika da shaguɓe ga ƴan soshiyal midiyan jam’iyyar APC na ƙasa, bisa zargin rashin basu kyakkyawar kulawa a taron da APC ta yi a Jos.
Masu amfani da Facebook da dama ne suka riƙa tsokaci da ke nuna cewar an fifita ƴan Kannywood a kan ƴan soshiyal midiya.
Wani abu da ya ƙara ƙarfafa wannan muhawara shi ne rashin ganin fuskokin wasu manyan ƴan soshiyal midiyan jam’iyyar na Arewa kamar su Rabi’u Biyora da Bashir Abdullahi El-Bash a wajen taron.
Ku kalli saƙonnin da wasu suka wallafa.
Daman dai an jima ana ƴar tsama a kan wannan batu, inda da dama daga ƴan soshiyal midiya ke zargin ƴan siyasa da nuna musu wariya, tare da fifita ƴan nanaye a kansu.
Ku meye ra’ayinku?
You must be logged in to post a comment Login