Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babu wani rikici a jam’iyyar APC – Kabiru Gaya

Published

on

Ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya,ya ce babu rikici a jam’iyyar APC ta Kano.

Sanata Gaya ya bayyana hakan a yayin taron manema labaran da ya jagoranta na ƴan majalisun tarayyar Kano 21 da ke goyon bayan Gwamma Ganduje.

Gaya yayi watsi da ƙorafin da wasu ƴaƴan jam’iyyar suka yi kan tsarin tafikarwarta Kano.

Saboda haka yayi kira ga shugaban rikon jam’iyyar na ƙasa Mai Mala Buni, da yayi watsi da ƙorafin da aka yi masa.

Sanatan ya ci gaba da cewa, duk wani abu da ya taso na jami’iyyar to a sanya kowa a ciki domin kansu a haɗe ya ke.

Wannan dai na zuwa ne Kwanaki kaɗan bayan da wasu ƴaƴan jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau suka yi ƙorafi kan rashin kyakkyawan tsari wajen gudanar da jam’iyya a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!