Labarai
Ana zargin Mele Kyari da Gowdwin Emefiele kan batan dabo na wasu kudade
Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Malam Mele Kyari da gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele, da su gurfana gabanta don yi musu karin haske, kan wasu kudade da suka kai naira tiriliyan uku da biliyan ashirin da hudu.
A cewar majalisar kudade ne da aka sayar da danyen mai a shekarar dubu biyu da goma sha hudu.
Shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar wakilai, Wole Oke ne ya aika da wannan tuhuma, biyo bayan rahoton da kwamitin ya karba daga ofishin babban mai binciken kudi na tarayya.
Tun farko dai kwamitin ya zargi shugaban kamfanin na NNPC, Malam Mele Kyari da kin amsa gayyatar da yayi masa, saboda haka ya ce, wajibi ne shugabannin biyu su gurfana gaban kwamitin don sanar da su yadda aka yi da kudaden.
You must be logged in to post a comment Login