Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana zargin shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus da almundahanar naira biliayn 10

Published

on

Sabon rikici ya kaure a jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya biyo bayan zargin da ake yiwa shugaban jam’iyyar Prince Uche Secondus da almundahanar naira biliyan goma kudaden da masu neman tsayawa takara a jam’iyyar suka bayar cikin shekaru hudu da suka gabata

Tuni dai daya daga cikin jagororin jam’iyyar ta PDP ya gurfanar da shugabancin jam’iyyar gaban hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ICPC.

Wanda ya shigar da karar shine Prince Kassim Afegbua wanda ya zargi jagorancin jam’iyyar karkashin jagorancin Uche Secondus da almundahanar naira biliyan goma wanda kudade ne da ‘ya’yan jam’iyar su ka biya don sayan form din takara daga shekarar 2017 zuwa bana

Sai dai yak e mai da martani kan zargin mai magana da yawun jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan ya bayyana zargin a matsayin zance marar tushe

A cewar Ologbondiyan jam’iyyar PDP ba ta samu wadannan kudade masu yawa da Prince Kassim Afegbua ya yi ikirari ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!