Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Najeriya za ta yi da na sani idan aka kori Pantami daga minista – Sheikh Gumi

Published

on

Fitaccen malamin addinin islaman nan da ke Kaduna Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya yi gargadin cewa, Najeriya za ta yi mugun da na sani matukar aka kori ministan sadarwa da bunkasa fasahar tattalin arziki, Dr. Isa Ali Pantami daga mukaminsa, sakamakon zargin da ake yi masa na alaka da ‘yan ta’adda.

A baya-bayan nan ne dai wasu ‘yan Najeriya ke ta kiraye-kirayen neman sauke Pantami daga mukaminsa.

Sai dai shehin malamin da ke Kaduna ya yin zantawa da gidan talabijin na Roots, ya ce, zargin da ake yiwa ministan ba gaskiya bane kuma bai kamata ma a rika tattauna shi ba.

‘‘Babu wanda ya isa ya musuluntar da duk mutanen duniya. Yesu Almasihu ya zo bai iya sanyawa duk kowa ya karbi addinin kirista ba. Babu wanda ya isa ya mai da Najeriya kasar musulmi ko na kirista’’ a cewar Sheikh Gumi.

A cewar Sheikh Gumi duk wanda ya san alakar Sheikh Pantami ya san ba dan ta’adda bane kuma ba ya alaka da su. Su kansu ‘yan ta’addar sun tsaneshi kuma sun sha neman hallaka shi. Saboda haka kasancewar sa minista daya ne daga cikin hanyoyin yaki da ta’addanci.

‘‘Ka nuna mini mutum daya da ya kashe. Bai kashe kowa ba. Sannan bai ba da umarnin kashe wani ba. Saboda haka kuyi watsi da farfagandar da ake yadawa akansa.’’ Sheikh Gumi.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!