Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Corona: Ku daina ziyartar kasashen Indiya, Brazil, Turkiya – Buhari ga ‘yan Najeriya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya da su kaucewa tafiye-tafiye zuwa kasashen Indiya, Brazil, Turkiyya da kuma Afirka ta Kudu, sakamakon yadda cutar Covid-19 ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.

Kwamitin yaki da cutar Corona na fadar shugaban kasa ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai ta bakin wani babban jami’inta Dr. Mukhtar Muhammad.

Dr. Mukhtar Muhammad ya ja hankalin jama’a da su rika bin matakan kariyar cutar sakamakon yadda take ci gaba da kara bazuwa a wasu kasashen duniya.

Matakan kariyar sun hada da bayar da tazara da sanya takunkumin rufe baki da hanci da wanke hannu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!