Connect with us

Labarai

Ana zargin wani matashi da hallaka matar yayan sa a Gusau

Published

on

Ana zargin wani matashi mai suna Aminu Bala dan kimanin shekaru 28 da hallaka matar yayan sa mai suna Hauwa’u Ilyasu ‘yar shekaru 27.

Wannan al’amari ya faru ne a unguwar Damba dake karamar hukumar mulkin Gusau babban birnin jihar Zamfara a daren ranar Lahadi.

Wakilin mu Abdullahi Salisu Faru ya zanta da wasu shaidun gani da ido kan al’amarin wadanda suka ce Aminu Bala ya zo da wuka inda ya sassareta a jiki kafin daga bisani ya arce.

A nata bangaren mahaifiyar mijin matar ta shaidawa Freedom Radio cewa an sanar da ita wannan labari mara dadin ji kuma yanzu haka ‘yan sanda sun shiga cikin lamarin.

Wakilin na mu yayi kokarin jin ta bakin mijin matar wanda ke kan hanya daga Abuja amma abin ya gagara.

Haka kuma munyi kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara amma har zuwa wannan lokaci da muke hada wannan rahoto abin ya ci tura.

Hotunan da wakilin mu ya aiko mana daga inda al’amarin ya faru.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!