Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaban majalisar gudanarwa na jami’ar Maitama Sule yayi murabus

Published

on

Shugaban majalisar gudanarwa ta jami’ar Yusuf Maitama Sule dake nan Kano Malam Sule Yahaya Hamma ya sanar da yin murabus daga mukamin sa.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Malam Sule Yahaya Hamma da ya aikewa sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji yace ya ajiye mukamin nasa ne bisa dalilai na kashin kai.

Cikin sanarwar Alhaji Sule Hamma yayi godiya ga gwamnati bisa goyon bayan da ya samu a yayin gudanar da aikin sa, tare da yin fatan alkhairi ga jami’ar.

Malam Suleh Yahaya Hamma shi ne shugaban majalisar gudanarwa na farko a jami’ar Yusuf Maitama Sule da aka nada a watan Mayu na shekara ta 2013.

Labarai masu alaka:

Jami’ar Yusuf Maitama Sule zata yi bikin yaye dalibai

Jami’ar Yusuf Maitama Sule za ta kashe sama da naira biliyan uku

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!