Connect with us

Coronavirus

Corona ka iya kashe kananan yara sama da 50,000 a Afirka – MDD

Published

on

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa annobar Covid-19 ka iya kashe karin 51,000 na yara ‘yan kasa da shekara biyar a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka daga nan zuwa karshen shekara.

Hukumar lafiya ta duniya WHO da asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun ce kalubalen da ya dabaibaye harkar lafiya da kuma rashin isasshen abinci mai gina jiki barazana ce babba ga lafiyar yaran a yankunan.

Wata sanarwa ta hadin gwiwa da hukumomin suka fitar a Amman, sun ce karin kididdigar da za a samu na mace-macen yaran zata shanye kusan kaso 40 na adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar Covid-19.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!