Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda sun bazama cafko wadanda suka kwakwale wa Almajiri ido

Published

on

 

Wasu mutane da ake zargin yan kungiyar asiri ne sun kwakwalewa wani Almajiri mai suna Yusuf Idanu a dajin kusa da garin Shuwarin dake yankin Karamar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa.

Lamarin dai ya faru ne a jiya Juma’a da rana bayan da Yusuf da ‘Yan uwansa suka tafi daji neman Itace, kamar yadda wasu makusantansa suka shaidawa Freedom Radio.

“Naga itacen sa a kofar wani kango sai na zagaya domin naga mekefaruwa sai na gansa cikin jini an yada shi a kongon.

Ko da muka jawo sa sai muka ga babu an Ƙwalele masa ido daya daga nan muka garzaya da shi asibiti ko da muka isa aka tabbatar mana da rasuwar sa”.

DSP Lawan Shisu Adam shi ne Jami’in hulda da jama’a na Rundunar yansandan jihar Jigawa yace sun sami labarin har ma tuni sun shiga farautar wadanda suka aikata wanan danyan aikin domin hukuntasu.

An ganshi a cikin daji a kwance a cikin jini mun kuma baza ma’aikatan mu domin binciko waɗanda suka aikata wannan aika aika

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!