Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana zargin wasu matasa sun hallaka wani matashi a Kano

Published

on

Wasu matasa sun hallaka wani matashi Mai Suna Zahraddeen Mukhtar ta hanyar caka masa wuƙa a ƙahon zuciya.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar a unguwar Sheka Gidan Gabas.

Ƙanin mahaifin marigayin Malam Aminu Haruna Sulaiman ya shaida wa Freedom Radio cewa, wasu matasa ne ƴan unguwar suka kira shi a waya, bayan ya fito kuma suka caka masa wuƙar.

“Munje asibitin Sheka daga nan muka ɗauki adaidata sahu domin mu kai shi babban asibiti, bayan an samu ƴan sanda, amma a hanya rai yayi halinsa” a cewar sa.

Ita ma ana ta ɓangaren mahaifiyar marigayin Malama Hadiza Isyaku wadda take cikin kaɗuwa ta shaida wa Freedom Radio cewa, babban abin da take buƙata shi ne abi mata haƙƙin ɗan ta.

Mun so jin ta bakin mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Kiyawa amma bai ɗauki kiran wayar da muka masa ba.

Sai dai dangin marigayin sun tabbatar da cewa, tuni ƴan sanda suka sahale musu su yi masa jana’iza wadda ake shirin aiwatarwa yanzu haka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!