Kasuwanci
Anchor Borrowers: CBN na bin manoma bashin sama da naira biliyan 378
Babban Bankin Najeriya CBN, ya ce, akwai sauran kudi naira biliyan 378 da miliyan 500 a hannun masu biyan bashi da suka amfana karkashin shirin Anchor Borrowers a cikin shekaru shida.
CBN dai ya gudanar da ayyuka miliyan 2 da dubu 300 karkashin shirin tare da bayar da lamunin kudi naira biliyan 497 da miliyan 200 ga manoma.
Amma a cikin rahoton tattalin arziki da Babban Bankin na CBN ya gabatar a shekarar 2020, ya bayyana cewa wadanda suka amfana da shirin, sun biya naira biliyan 118 da miliyan 700 kacal, ya zuwa karshen iya lokacin da aka kayyade musu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da shirin bada bashin a ranar 17 ga watan Nuwamban 2015 a wani yunkuri na sauya salon bashin kudaden kayayyakin abinci da Najeriya ta kasa biya.
You must be logged in to post a comment Login