Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da sauke wasu daga ciki masu rike da mukaman siyasa

Published

on

Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya amince da a sauke dukkanin masu rike da mukaman siyasa a jihar daga jiya juma’a.

Babban daraktan yada Labaran gwamnatin jihar Ismaila Uba Misilli, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya juma’a.

Sanarwar tace ‘saukewar bata shafi shugabannin riko na kananan hukumomi ba, saboda haka za su ci gaba da rike mukamansu har zuwa karewar wa’adinsu a ranar 19 ga watan Yuni mai zuwa’.

Kazalika Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma amince da murabus din shugaban ma’aikatan jihar Gombe Alhaji Bappayo Yahaya, inda ya amince da nadin babban sakatare ga Gwamna Ahmed Kasimu Abdullahi a matsayin mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar’.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!